SINADARIN MA'AURATA NA MUSAMMAN DON FARIN CIKIN MA'AURATA
Wannan hadin yana taimakawa wajen jimawa a jiki, kara kuzari, da inganta martaba mace a idon mijinta.
Ga abin da ake bukata:
Sinadarin Hadin:
Furen zogale
Zanjabil
Habba
Garin raihan
YADDA AKE HADAWA:
Dakesu dakyau a guri daya.
Dibawa karamin cokali.
Hadawa da zuma, sha da safe da yamma.
Hadin Matan Masar da Matan Sudan
Wannan hadin yana inganta ni'ima, gyara aure, da sa nishadi ga masoya. Ga abubuwan da ake bukata:
Kankana mai kyau
Zuma
Raihan
YADDA AKE HADAWA:
Yayyan kankanar, zuba a kofi.
Saka zuma da madarar ruwa da garin raihan.
Sha safe da yamma.
RASHIN SHA'AWA
Ga mata da ke fuskantar matsalar rashin sha'awa ko jin dadin saduwa, wannan hadin zai taimaka:
Zangarniyar zogale da ya'yanta gadaya
Karanfani
Citta
Masoro
Kinba
YADDA AKE HADAWA:
Dakesu su zama gari.
Sha a shayi safe da yamma.
Ni'ima Sinadari Mai Dadi
Wannan hadin yana taimakawa wajen inganta ni'ima da jin dadi:
Ya'yan zogale
Kankana
Yadda ake hadawa:
Dakesu suyi laushi.
Sha da nono safe da yamma.
Don Farin Cikin Ma'aurata
Hadinnan yana kara farin ciki a cikin aure, yana inganta sha'awa:
Kankana mai kyau sosai (yayyankata)
Ya'yan zogale
Kumasoriyya ta asali
Ayaba mai kyau sosai
YADDA AKE HADAWA:
Dakesu suyi laushi.
Dibawa karamin cokali, hadawa da kankanar, ayaba da madara.
Sha sau biyu a rana, safe da yamma.
Don Magance Zafin Saduwa
Wannan hadi yana taimakawa wajen magance zafin saduwa ko rashin sha'awa:
Dabino
Garin ridi
Garin habba
Garin raihan
YADDA AKE HADAWA:
Saka zuma lita daya, hadasu wuri daya.
Sha cokali daya a ruwan shayi, safe da yamma.
@By Chef Oum Aslam ✍🏻✍🏻
0 Comments