MUHIMMAN SIRRINKAR MALLAKAR MIJI
▪ yana da kyau ki kasance kullum cikin gano abin da mijinki yake so da abin da baya so.
▪ ki kasance mara kwadayin abin hannunsa.
❀ ki kasance cikin tsaftace muhallinki, gidanki ko jikinki.
❀ ki kula da iyayensa da ‘yan’uwansa da abokansa.
❀ ki kasance mai tsoron Allah cikin dukkanin al’amuranki.
❀ kada ki zama mai yawan shige-shige na makota.
❀ ki sani cewa kece inuwar hutawarshi da jin dadinshi.
❀ idan mai mata kika aura ki yi biyayya ga matarshi, kada ki ce wai lokacin daya zaki raba shi da uwargidansa, ki rike masa ‘ya’ya kamar ‘ya’yan da kika haifa.
❀ ki kasance cikin gano wani sabon salo-salo na wasanni a tsakaninku.
❀ ki kasance kullum a jikin mijinki, ki dinga nuna masa kullum ke yarinya ce, kina yi masa shagwaba koda kina shekara 50.
❀ kada ki dinga yin aikin da namiji yake yi ya zama na kullum, da an ganki an ga ‘ya mace.
❀ kada mijinki ya gano kina da mita ko saurin fushi.
❀ kada ki zama mai bayyana sirrinki a social media ga kawaye.


0 Comments