Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

DALILAN DA YASA MUTANE KE YAWAN KAMUWA DA MURA DA TARI A LOKACIN SANYI


 DALILAN DA YASA MUTANE KE YAWAN KAMUWA DA MURA DA TARI A LOKACIN SANYI 


A lokacin sanyi (cold season), mutane da yawa kan fara fama da mura, tari, zazzabi, ciwon makogwaro, da cunkoson hanci. Amma ka taɓa tambayar kanka me yasa hakan ke faruwa? 


A hakikanin gaskiya, ba wai sanyi kansa ko amfani da ruwan sanyi ne ke kawo mura ba — amma sanyi yana sauƙaƙa wa ƙwayoyin cuta (virus) damar yaduwa cikin sauƙi Saboda wadannan dalilan


1.ƘWAYOYIN CUTAR SUNA YAWAITA A LOKACIN SANYI: A lokacin sanyi, ƙwayoyin mura da tari (musamman rhinovirus da influenza virus) suna rayuwa daɗe a cikin iska da jiki. Wannan yana sa su fi yaduwa cikin sauƙi daga mutum zuwa mutum.


2• ISKA MAI SANYI TANA BUSAR DA HANCI DA MAKOGWARO: Lokacin sanyi, iska tana da ƙanƙantar danshi (dry air). Wannan busasshiyar iska tana sa bangon hanci da makogwaro su bushe, kuma hakan yana rage kariya daga ƙwayoyin cuta. Idan mucous (ruwan hanci) ya bushe, ƙwayoyin cuta suna samun damar shiga cikin jiki da sauri.


3.MUTANE SUNA ZAMA A GURI DAYA: A lokacin sanyi, mutane da yawa suna zama a cikin gida ko wurare masu ɗauke da mutane, kamar ofis, makaranta, ko masallatai. Wannan cunkoso yana taimaka wa cututtuka su wuce daga mutum zuwa mutum cikin sauƙi.


4 GARKUWAR JIKI TANA RAUNI: Rashin isasshen bacci, rashin cin abinci mai gina jiki, da ƙarancin rana (vitamin D) a lokacin sanyi na iya rage ƙarfinsa wajen yaƙar ƙwayoyin cuta. Hakan yana sa mutum ya fi kamuwa da mura da tari.


5.RASHIN KARIYA DAGA SANYI: Wasu mutane basa sanya kaya masu dumi, ko suna wanka da ruwa mai sanyi da safe. Wannan yana sa jiki ya saki zafi da sauri, yana barin damar cututtuka su kama mutum.


YADDA ZA KA KARE KANKA 

✅ Ka rika sanya kaya masu dumi (rigar sanyi, hula, safa, da takalmi masu rufe ƙafa).

✅ Ka sha ruwa da yawa — ko da ba ka jin ƙishirwa.

✅ Ka ci abinci mai gina jiki da ke ƙarfafa garkuwar jiki

✅ Ka guji zama a wurin da mutane ke yawan tari.

Masu Bukatar Magungunan Mu irinsu Original sabaya Magungunan Mata Dana Gyaran Breast Hips Karin kiba Garin kunun Yara set din Ni'ima Matsi da Infection kayanmu 100% Natural ne muna aikawa kowani gari Cikin Aminci Inshallah (07062950801)_ (08084726875).

Daga Chef Oum Aslam✍️✍️



Post a Comment

0 Comments