(Daga Jaridar Ciki Da Raino)
A yau zamuyi takaitaccen bayani ne akan tambayar da aka saba yi min dangane da motsin jariri da kuma lokacin da yake fara motsi.
Yawanci, za ki fara jin motsin jaririnki a tsakanin sati na 16 zuwa na 22 na goyon ciki. A wannan lokacin, motsin jaririn na iya kasancewa ne da kadan-kadan wato ba sosai ba.
Amma daga baya idan ciki ya kara tsufa, jaririnki zai fara tsara yadda zai dinga motsawa na karan kansa wanda uwa zata fara gane lokacin har kuma ta saba da hakan.
Wannan tsarin motsi nasa na iya zama babbar alamar dake nuna cewa jaririnki yana cikin lafiya.
Motsin jaririn zai haɗa da nau'ikan motsi daban-daban kamar bugun kafa, jujjuyawa, lanƙwasawa, da motsi mai kama da tsalle-tsalle. Daga baya, motsin zai kasance na yau da kullum, kuma ya kamata ki ji su kullum, idan har jaririnki yana cikin koshin lafiya.
A duk lokacin da kika je awon ciki, mai kula da lafiyar ciki (midwife) za ta tattauna da ke game da tsarin motsin jaririnki. Idan aka sami wani canji, musamman raguwar motsi ko jariri ya daina motsawa kamar yadda kika saba ji, wannan na iya zama alamar cewa jaririn yana buƙatar a duba lafiyarsa.
WOMEN HEALTHCARE✍️
0 Comments