MASU FAMA DA RASHIN HAIHUWA MAZA DA MATA KUZO GA MAGANI DA YARDAN ALLAH KU JARRABA SHI.
NEMAN HAIHUWA
Masu fama da matsalar rashin haihuwa saboda ƙaranci ko raunin ƙwayoyin halittan maniyyi ko wata matsala da ta shafi sanyin mara (infection/STI) ko mahaifa kamar PID, PCOS, Ovarian Cyst, Tube blockage ko matsalar planning har da tsakuwar ƙoda
Agwada wannan maganin na tsawon sati biyu insha Allah za'a dace.
ABUBUWAN DA ZA'A NEMA
1- Ganyen mangworo
2- Ganyen Gwanda
3- Habbatussauda
4- Tafarnuwa
5- Kananfari
6- Citta
7- Zuma
8- Idan rauni ko ƙarancin ƙwayoyin halittan maniyyi ne ahaɗa da Fijil
YANDA ZA'A HAƊA
Asamu ganyen mangworo guda 5, ganyen gwanda kamar faɗin tafin hannu ɗaya, ƴaƴa ko garin Habbatussauda chokali 3, Tafarnuwa ƙwollo ɗaya, garin kananfari chokali ɗaya, Fijin chokali ɗaya sai ɗanyen citta dadai misali (a kankare a jajjata).
Za'a zubasu duka a tukunya asa ruwa liter 5 da rabi (pure water leda 11) adafa yadahu sosai idan ya huce atace asa zuma chokali 10.
Za'a dinga shan rabin kofi safe da rana da dare na tsawon sati biyu.
TAMBIHI:
Wannan maganin maza ma zasu iya amfani dashi sannan Kafin afara amfani da wannan maganin mutum yafara zuwa asibiti domin a tabbatar masa da bunda yake damunsa.


0 Comments