YADDA AKEYIN HADADDIYAR KUNUN COUS-COUS
Assalamu alaikum, barka da war haka, a yau dai wannan filin namu yana dauke ne da yadda akeyin Kunun couscous.
KAYAN DA ZA KI TANADA
1. Cous-cous
2. Sikari ko zuma
3. Madara
4. Tufa
5. Ayaba
6. Filebo na vanilla
YADDA ZA KI HADA KUNUN
Ki sami madarar gari ko ta ruwa, duk wadda ki ke da ita, idan ta gari ce sai ki kwaba ta da ruwa ta yi tsululu sai ki dora akan wuta, idan ta tafaso sai ki kawo kus-kus din ki ki zuba a ciki ki ringa juyawa domin ka da ya dunkule. Idan kin zuba iya yawan da ki ke so sai ki cigaba da juyawa har zuwa minti biyar. Idan ya dahu kuma kaurin ya yi miki sai ki sauke daga kan wuta ki zuba sikari, ki yanka tufa da ayaba ki saka sikari ko kuma zuma duk wanda ki ke so, sannan ki kara madara, ki zuba filebo mai kamshin banila ki juya, shi kenan sai sha.
Ki na iya yi da safe domin yara su sha kafin su tafi makaranta, haka kuma kina iya domin ki bawa yaro dan yaye. Amma idan yaro dan yaye ne ba sai kin saka tufa da filebo ba a ciki ba, ita ma kuma ayabar sai ki dame ta, kuma zai fi idan ki ka saka zuma a ciki ba sikari ba.
Idan kina so iya saka wasu kayan marmarin ba lallai sai ayaba da tufa ba, kina iya saka abarba ko kankana ko gwanda ko dai duk wani kayan marmari da ki ke da sha’awar sakawa a ciki ko kuma iyalanki suke son ci.


0 Comments