Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

ALAMOMIN SHIGAR CIKI NA FARKO DA MATA KE FARA GANI


 ALAMOMIN SHIGAR CIKI NA FARKO DA MATA KE FARA GANI



Wasu mata kan fara ganin wasu alamomi tun farkon lokacin da ciki ya shiga. 


Duk da haka ba dole ba ne kowace mace ta ga dukkan alamomin.


Ga wasu daga cikin su:


1️⃣ Rashin ganin al’ada a lokacin da ya kamata ta zo.

2️⃣ Ciwon nono ko nauyin nono.

3️⃣ Tashin zuciya ko amai musamman da safe.

4️⃣ Yawan jin gajiya ko kasala.

5️⃣ Yawan fitsari fiye da yadda aka saba.

6️⃣ Canjin dandano ko jin ƙamshi sosai.

7️⃣ Dan zubar jini kaɗan a farkon ciki.

8️⃣ Ɗan ciwon mara kamar na al’ada.


⚠️ Idan mace ta fara ganin irin waɗannan alamomi, yana da kyau ta yi gwajin ciki (PT) ko ta je asibiti domin tabbatarwa.


📢 Ku dinga zuwa asibiti domin kula da lafiyar ku da ta jariri.



Post a Comment

0 Comments