HANYOYI GOMA 10 DA ZAKI BI KI MALLAKI MIJINKI CIKIN RUWAN SANYI.
Idan kina son mijinki ya zama Mijin hajiya na bugawa a jarida, ga wani sirri zan baki...
Maganar gaskiya wacce dole ki hadiye ta ita ce; Mallakar Namiji ba a gidan Boka ko malamin tsubbu yake ba. Zuciyar Namiji tana da makulli guda daya kacal a duniyar nan: KWANCIYAR HANKALI.
Kafin ki ci gaba da kashe kudinki wajen neman asirin farin jini, kalli wadannan hanyoyi 10 na halas wadanda idan kika rike su, wallahi kin gama mallakar mijinki:
1. Bashi Cikakken Girmansa:
Namiji yafi son mace mai yi masa biyayya da girmamawa akan mace mai yawan nuna masa soyayyar da bata da ladabi. Girmama shi a matsayin shugaba, zai mayar da ke sarauniya.
2. Tausayawa Aljihunsa:
Daina gasa da kawayenki wajen sanya shi yi miki abin da yafi karfinsa. Matar da take rufa wa mijinta asiri a lokacin da bashi da shi, ita ce wacce baya taba mantawa da ita a ranar da ya samu.
3. Koyi Yin Shiru Lokacin Fushinsa:
Mafi girman kuskuren mace shine mayar da martani a lokacin da ran mijinta a bace yake. Namijin da ya mallaki kansa, baya fada da mace mai yin shiru tana bashi hakuri.
4. Kula Da Tsaftar Jiki Da Muhalli:
Kwalliya da kamshi ba na fita biki ba ne kawai. Ki zama mai daukar hankalinsa a kowane lokaci a cikin gidansa. Tsafta tana sace zuciyar Namiji fiye da kalaman soyayya.
5. Rike Sirrin Gidanki:
Duk matar da take kai kukan mijinta wajen kawaye ko a Social Media, tana zubar da kimarta ne. Sirrin gidanki ya zama a kulle, ki zama asirin mijinki, zai amince daki fiye da kowa.
6. Ciyar Da Shi Da Kyau:
Hanyar zuciyar Namiji tana farawa ne daga cikinsa. Ki kware wajen yi masa girki mai dadi da tsafta. Namiji yana alfahari da matar da ta iya tsara masa abinci a kan lokaci.
7. Yaba Kokarinsa:
Koda dan abin da ya kawo kadan ne, ki nuna masa godiya daga kasan zuciyarki. Namiji yana kara kaimi ne idan yaga ana yaba kokarinsa, amma korafi kashe masa gwiwa yake yi.
8. Nisantar Kawayen Banza:
Kada ki bari masu ba ki shawarar "Kada ki bari ya raina ki" su ruguza miki gida. Kawayen da basa girmama mazajensu ba zasu taba ba ki shawarar da zata gina naku ba.
9. Kula Da Iyayensa Da Danginsa:
Matar da take girmama iyayen mijinta da 'yan uwansa, tana siyan zuciyarsa ne ba tare da ya sani ba. Baya taba bari a ci zarafinki idan yasan kina kyautata wa nasa.
10. Addu'a Da Neman Zabin Allah:
Babu wani makami da yafi addu'a karfi. Ki dinga taya shi da addu'ar neman kariya da budi a kasuwancinsa. Matar da take rokon Allah akan mijinta, Allah Zai karkato da zuciyarsa gare ta.
Yar uwa, Namiji yaro ne mai babban jiki. Idan kika lallaba shi da wadannan abubuwan, wallahi zaki sarrafa shi cikin ruwan sanyi ba tare da kin yi asarar mutuncinki ko addininki ba.
Masu Bukatar hadaddun Magungunan Gyaran Nono Breast Karin Hips Karin kiba set din Ni'ima Matsi da infection flusher na sliming Rage Tumbi da kiba original sabaya Duk Available Muna Aika kayanmu kowane gari inshAllah (07062950801)


0 Comments