YADDA AKEYIN DODO GIZZARD WATO STICK MEAT NA ZAMANI ME KYAU GA DADI DONCI KO HIDIMAR SALLAH


STICK MEAT

     INGREDIENTS 

  • Gizzard (qundun kaza)
  • Plantain,
  • Oil
  • Toothpick (tsinken sakace)
  • Tarugu,
  • albasa,
  • tattasai
  • tafarnuwa.
  •  Seasonings da spices.

PROCEDURE:

A tafasa qundun kaza tare da spices, in ya nuna sai a soya shi sama-sama, a yayyanka qanana. Sannan a yanka agada a masa yanka 'yan madaidaita ta, sai a soya shi yayi golden brown. Daga nan a jajjaga albasa, tarugu, tattasai da tafarnuwa. Sai a sa mai kadan a tukunya a zuba a soya shi. Sai a juye naman a ciki a jujjuya.

Daga nan sai ki fara shirya su a tsinke har ki gama. Dadi kuwa sai kin bani Labari. Note: Zaki iya yi ki haďa su ba tare da kin sakasu a tsinke ba. Sai a jujjuya su duka wuri đaya kiyi serving. Sannnan zaki iya yi a dogayen tsinken da suka fi wannan tsayi.