Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

HANYOYIN DA AKE BI DOMIN SAMUN WARAKA DAGA MATSALOLIN JINNU/SIHIRI/SAMMU/ DA MAITA


 HANYOYIN DA AKE BI DOMIN SAMUN WARAKA DAGA MATSALOLIN JINNU/SIHIRI/SAMMU/ DA MAITA:



Abune sananne awannan Zamani na faruwar cututtuka kala daban-daban da suka addabi mutane, musamman matsalolin Jinnu da na Sihiri/Sammu.


A wannan Bayanin da zamuyi Insha Allah zamu zayyano hanyoyin da yakamata mutum yabi wurin Samun Magani akan wadannan matsaloli ko nemawa kansa kariya da Iyalansa akan cututtukan da Jinnu ke sanyawa mutane ta sanadiyar shigar da sukeyi ajikin mutane kokuma shafar da sukeyiwa mutane ta sanadiyar sammu/Sihiri.


Wadannan hanyoyi da akebi abisa karantarwar musulunchi sun kasu kashi 5, sune kamar haka:


1. AZKAR: Duk Wanda yake neman kariyar Allah akan kowacce irin musiba dakuma son samun daukaka duniya da lahira kokuma neman waraka daga wata jarabawa toh dolene mutum ya yawaita ambaton Allah, musamman wadannan lokutta; Lokacinda aka tashi daga barci, bayan sallar Asuba, Bayan sallar La'asar, lokacin kwanciya barci, yayin da mutum zai fito daga gida ko zai shiga.

Dukkan wadannan lokuttan akwai karantarwar da Musulunchi yayi na yadda za'a ambaci Allah a wadannan lokutta. Kuma kiyaye hakan babbar Nasarace arayuwa dakuma kariya daga dukkan shedanu na mutane da Aljannu.


2. TOFI ACIKIN RUWA: Akwai ruwayen da ake amfani dasu wurin karanta Ayoyin Alkur'ani da Addu'o'i(Ruqyah), Sai marar lafiyar yasha, kokuma shi marar lafiyar yakarantawa kansa. Kuma koda mutum lafiyarsa lau zai iya yinsu domin neman tsarin Allah da kariyarsa.(zamu bayyana su a kasidarmu ta gaba).


3. MAGANI:

Shan Magani abune da musulunchi yayi umurni da shi, kamar yadda dama dukkan musulmi yayi imanin babu wata cuta da batada magani Sai dai Wanda ya sani ya sani, Wanda kuma bai sani ba Sai ya nemi sani.


Akwai magungunan da Addinin Musulunchi ya bayyana amatsayin magunguna ne na larurori daban daban kuma har a yanzu binciken masana likitanci sun tabbatar da hakan, Sai dai kawai a sauyawa maganin sunansa ko kalarsa, amma dai wannan maganin ne da Musulunchi ya bayyana. Donhaka, duk mai neman maganin cututtukan Jinnu da na Sihiri, ko neman kariya daga dukkan wadannan matsaloli akwai su kuma insha Allah zamu zayyano su.

Daga cikin wadannan magungunan akwai wadanda ake Sha, shafawa, Turarawa, Shaqawa dakuma Wanka.


4. KIYAYE DOKOKIN ALLAH:

Babu yadda za'ayi ace kana sabon Allah dare da rana kana sabawa dokokinsa kuma kace kana neman kariyarsa da tsaronsa kokuma kace kana son samun Sauki daga aukuwar cututtuka.

Don haka, kiyaye dokokin Allah S.W.T da kiyaye Ibadah cikin lokaci, sune zasu taimakawa rayuwarka wurin samun saukin musibu da kwanciyar hankali.


5. TSAFTA: 

Tsafta wajibace ga Mutum Musulmi namijine ko mace, yaro ne ko Babba, donhaka duk Wanda zai kiyaye tsaftar jikinsa da ta muhallinsa, hakika ya nemawa kansa babbar kariya daga dukkan wasu cututtuka na rayuwa koda kuwa ta Jinnu ce ko ta sihiri insha Allah.


Masu Bukatar Magungunan na Gyaran Nono wato Breast Hips Karin kiba Magungunan Mata da Original sabaya infection flusher set dana Rage Tumbi da kiba duk Muna dasu available Muna Aika kayanmu kowane gari insha'Allah 07062950801 or 08084726875



Post a Comment

0 Comments