Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

MENENE AMFANIN GWAJI GENOTYPE KAFIN AURE KUNUTSU KU KARANTA MUHIMMIN BAYANIN SOSAI


MENENE AMFANIN GWAJI GENOTYPE KAFIN AURE KUNUTSU KU KARANTA MUHIMMIN BAYANIN SOSAI 


Kafin naje kan amfanin gwajin bari na danyi matashiya akan shi GENOTYPE din;


 Genotype test wani gwaji ne da akeyi domin gano mutumin da ke dauke da ciwon sickler, ko wanda bashi dauke da ita. 

Acikin ciwon sickler akwai kashe-kashe na jinane kashi uku;

AA, AS & SS


AA: shi mai dauke da wannan nau'in jini baya dauke da sickler kuma yayanshi bazasu iya gadar sickler ba(SS)


AS (Carrier): Shikuma mai wannan nau'in yana dauke da sickler amma bata nuna alama, amma kuma zai iya haifan yaya masu sickler idan ya auri mai kalar jini AS ko SS.


SS(sickle cell): shikuma mai wannan nau'i shine wanda yake dauke da sickler kuma tana nuna alama lokaci zuwa lokaci wanda ya hada da zazzabi mai zafi, matsanancin ciwon jiki dana gabobi, saurin kamuwa da cuta(infection).


AA vs AA: wannan shine hadi mafi inganci ba tare da tunanin zaa haifi sickler, duk yayan da zasu haifa zasu kasance 100% AA ne kawai.

AA vs AS: Shima wannan hadin bashi da wata matsala, yayan da zasu haifa akwai yiwuwar 90% zasu kasance AA while 10% zasu kasance AS.

AA vs SS shima wannan babu matsala domin duka yayan da zasu haifa zasu kasance 100%AS.


 AS vs AS, wato daga nan qalubalen ya fara domin kuwa wannan hadin akwai yiwuwar su kasance AA, AS ko SS ya danganta da kwayar haliitar da dan ya dakko.Wannan hadin baa sonshi.


AS vs SS, shikuma wannan hadin yan zasu kasance As da SS ne kawai(75%SS, 25%AS)


SS vs SS, wannan hadin zai kasance 100% yayan da zasu haifa SS(sickle cell).

  Yana da matuqar amfani kowa yasan genotype nashi tun kafin su fada relationship.

sabida genotype abune da baya taba canzawa.


Tsokaci na shine kada soyayya ta rufe maka/miki ido kukasa rabuwa da juna, gara kuyi kukan rabuwa da wahal halun da zaku shiga idan kuka haifi sickler, ba qaramin tashin hankali ne gareku ba, sannan yammata a kula kada zafin soyayya ya rudeku kuce kun yarda ayi auren zaku haquri da haihuwa, idan kuma hakan ta kasance so let him go for vasecto.



Post a Comment

0 Comments