AMFANIN RUWAN KUBEWA GA MACE (Water Okra–Okro Water) IDAN KE MACACE KITSAYA KI KARANTA ZAI MATUKAR AMFANEKI
Ruwan kubewa yana da matuƙar amfani ga lafiyar mace, musamman ma dangane da lafiya ta ciki da waje. Ga wasu manyan amfaninsa:
🌿 1. Yana Taimakawa Lafiyar Mara da Narkar da Abinci
Ruwan kubewa yana da sinadaran fiber masu yawa, wanda ke taimakawa wajen:
Rage kumburin mara
Sauƙaƙe narkar da abinci
Hana kumburin ciki da zafin mara (cramps)
💧 2. Yana Kara Ruwa a Farji (Lubrication)
Ga mata da ke fama da bushewar farji:
Ruwan kubewa yana taimakawa wajen samar da danshi na halitta
Yana rage jin zafi ko ƙaiƙayi yayin kusanci
🤰 3. Yana Taimakawa Haihuwa da Ciki
Ana alakanta ruwan kubewa da kawo sauki lokacin nakuda
Yana ƙara lafiyar mahaifa da rage tsoro ko radadi lokacin haihuwa
Yana iya taimakawa wajen ƙara haihuwa (fertility) a wasu mata
💆♀️ 4. Yana Kyautata Fata da Gashi
Yana hana fata bushewa da fashewa
Yana ƙara hasken fata da rage kuraje
Ruwan da aka sarrafa da kyau yana taimakawa wajen gyaran gashi
🩸 5. Yana Rage Hawan Jini da Zafin Jiki
Ga mata da ke fama da hawan jini lokacin haila ko ciki, yana taimakawa daidaita jini
Yana da sinadarai masu rage inflammation da oxidation
🩺 6. Yana Taimaka wa Masu Ciwon Suga da Jimewar Jiki
Yana taimakawa wajen daidaita sukari a jini
Ga mata masu jin gajiya ko rauni a jiki, ruwan kubewa na ƙara kuzari
🧪 YADDA AKE HADA SHI
Abubuwan Bukata:
Kubewa sabuwa (5-6)
Ruwa (1-2 cups)
Yadda Ake Yi:
1. A yanka kubewa danye (banda dahuwa)
2. A jefa a cikin ruwa a bar shi dare ɗaya (8-12hrs)
3. A tace ruwan, a sha safe da yamma
> Lura: Kada a saka sugar ko flavour. A sha ruwan danye ne kawai.
⚠️ Gargadi:
Kada a sha fiye da sau biyu a rana
Idan kina da wani ciwo ko kina da ciki, ki tambayi likita kafin amfani
0 Comments