ABUBUWAN DA KOWACE MACE YAKAMATA TANADASU DOMIN KULA DA KANTA AKODA YAUSHE
1. Farin Miski
Amfani: Ana amfani da shi wajen samun kamshi mai daɗi a jiki da al’aura. Hakanan yana hana wari da haifar da kwanciyar hankali.
2. Mai da Ƴaƴan Hulba
Amfani: Hulba na da fa'ida wajen kara ni'ima da ƙara lafiyar gaba, musamman ga matan aure.
3. Kananfari (Clove)
Amfani: Yana tsarkake gaba, yana hana warin gaba, kuma yana ƙara daɗin saduwa ga ma'aurata.
4. Tazargaɗe
Amfani: Wani nau’in ganye ne da ke maganin infections da kuma kara lafiyar al'aura.
5. Bagaruwa
Amfani: Ana amfani da ita wajen ƙara laushi da matse gaban mace. Yana taimakawa da tsarkin jini.
6. Gishiri (gishirin tsafta)
Amfani: Ana amfani da shi wajen wanke al’aura ko don magance wari da kumburi, da safe ko bayan haila.
7. Auduga
Amfani: Tana da amfani sosai wajen tsafta, musamman lokacin haila ko bayan wanka.
8. Zuma (ga matan aure)
Amfani: Zuma tana ƙara kuzari da ni’ima, ana amfani da ita a abinci ko a haɗin gyaran gaba.
9. Tiraren Humra
Amfani: Wannan na jawo ƙamshi a jiki da tufafi. Hakanan yana ƙara wa mace kwarjini da kyan fata.
10. Garin Lalle
Amfani: Lalle yana wanke fata, yana hana ƙuraje, yana ƙara ɗan kyalli da kyan fata.
11. Ganyen Magarya
Amfani: Ganyen yana da amfani wajen wanke gaba, yana kashe cututtuka kuma yana hana wari da ƙuraje.
12. Kwalli
Amfani: Kwalli yana ƙayatar da idanu, yana da amfani ga lafiyar ido kuma yana ƙara wa mace kwarjini.
0 Comments