MIJINA YAI ALƘAWARIN IDAN NA ƘARA HAIFO MASA ƳA MACE SAI YA SAKENI KUNUTSU KU KARANTA BAYANIN SOSAI YANA DA MATUKAR AMFANI GA KOWA
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
Saƙon wata baiwar Allah kenan dake cikin damuwa, inda ta nemi na taimaketa idan akwai yadda zatai ta sami ɗa Namiji.
Wato yayin da rashin mutuncin wasu daga cikin Magidanta ya tashi sai ka sami mutum ya tasa Matarsa gaba yana mata gargaɗi akan idan ta kuskura ta kuma haifo masa ƴa Mace sai ya sake ta. Ko ya riƙa ma ta barazanar azabtarwa tare da tsangwama, gami da nuna halin ko in kula idan ya fahimci ƴa Mace take shirin haifa.
Toh amma albarkacin aure wasu kanci wanda yai hani da Mace tai sa-in-sa da mijinta. Banda haka Mace nada ikon kare kanta anan. Ba wani namiji da ya cancanci a rarrashesa akan wannan al'amarin, wai azo ana bashi hakuri don an haifi Mace alhalin inda mai laifi kan hakan shine.
Mu ajiye zancen ma ai Allah ne ke bada haihuwar abinda yaso ga wanda yaso. Tunda ko annabawa akwai masu ƴaƴa Mata zallah kamar Annabi Shu'ayb, akwai me ƴaƴa Maza zallah kamar Annabi Yusuf, akwai kuma me mixed na Mata da Maza kamar Annabin mu Muhammad (SAW). To amma duk mu ture wannan gefe, Ni bame wa'azi bane. Mu dauki ilimin haihuwar zallah a likitance kurum.
Zan so duk wani ɗa Namiji ya sani cewa; duk jinsin jaririn da kaga an haifa maka walau Mace ko Namiji tohfa daga gareka ne! Ƙwarai da gaske, kai ka samar dashi.
Mace don kurum tana Mace hakan bashi ke nuna ita ke samar da Macen ba. Namiji shine ke samar da Macen
BARI NAI MUKU DALLA-DALLA
Tun fil'azal Allah [SWT] ya tsara ƙwayoyin halittun jinsi kuma ya bambanta alamunsu... Ta yadda duk halittar dake ƙwai ko ɗaukar ciki ya zamto an mata alama ta "X" dake nuna ita Mace ce. Yayin da halittar da bata ƙwai, Saide tai Barbara asami ci akai mata alama da "Y" wanda ke nuna Namiji.
Toh wani hanzari anan shine: Duk wanda zaka gani a duniya Mace ce ta haife sa, inkaga namiji baka kokonton cewa Mace ce ta haife sa, haka in kaga Mace itama Mace ce ta haifeta... Dalilin haka sai ya xamto kowa yana da Kwafin halittar Mace tare dashi.
Wato kowacce Mace "X" tana da copy na Mahaifiyarta Mace "X" wanda ya maida ita "XX" Shima kowanne namiji "Y" yana da copy na Macen data haifeshi wanda hakan yasa ya mallaki "XY"
Don haka ita Mace dama ƙwanta "X" shine alamarta, baza ataɓa samunta da "Y" ba.
Idan aka sami mu'amala auratayyar da zai kai ga samun juna biyu... Zai xamto kowannensu ya saki Copy ɗaya na jinsinsa... Wato Mace ta saki 'X' tunda koma ya aka juya 'XX' ce, yayin da shi kuma Namiji zai iya sakin Copy ɗin "X" da ya samo daga mahaifiyarsa ko kuma ya saki "Y" alamar jinsa, tunda mun ji shi "XY" garesa, zai iya sakin kowanne.
KUN GA KENAN
Matukar kun fahimci wancan bayanin na samu to zaku gane cewa:
1- Idan aka sami ciki ya xamto an haifi ƴa Mace Toh hakan na nufin bayan UWA ta saki Copy ɗinta "X" wanda yake permanent, to UBA ma Copy ɗin "X" ya saki, wanda yasa aka sami X guda biyu wato "XX" dake nufin FEMALE CHILD. Kunga daga namijin ne da ya saki "X" mai makon "Y" ɗinsa.
2- Idan kuma aka sami ciki aka haifi Namiji Toh ita de Mace bata canzawa tunda ƙwai gareta, don haka ta saki Copy ɗinta na "X" shi kuma Namiji ya saki Copy ɗin "Y" sai aka sami X da Y sun haɗu aka haifar da "XY" wato MALE CHILD
Don haka wannan jahilcin da son zuciya na wasu Mazan muna fatan zai zo ƙarshe su gane cewa Macen nan fa sune da laifin samar da ita idan harma suna ganin hakan matsayin laifi.
Kuma wani abu ma shine "Y" chromosome din bai kai X na macen nauyi ba, yafi sauri da karsashi, amma duk da haka ka gaza sakinsa Saide "X" amma har kake da baƙin cin zarafin wani.
KOWANNE NAMIJI YA SANI
Namiji shike samar da jinsin Baby walau Mace ko Namiji... Duk copy din da ka saki shi za'a samu, don haka kai za aiwa gargaɗi idan ka kuskura ka qara haifo Mace to ranka sai ya ɓaci...😀 Mutumin kawai.
Gender is determine by Father, Not a Mother. Ba ruwan Matarka, tun a halitta ita dama Mace ce "XX" kake aure ba Namiji ba "XY".
Don Allah a yaɗa wannan ilimin, wallahi Maza na bukatar wayar dakai, ana yawan samun wannan jahilcin.
0 Comments