Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

WASU JERIN MUHIMMAN ABINCIN DA SUKE KARAWA MATA MASU SHAYARWA RUWAN NONO INGANTACCE


WASU JERIN MUHIMMAN ABINCIN DA SUKE KARAWA MATA MASU SHAYARWA RUWAN NONO INGANTACCE 


Abinda ya fi muhimmanci wajen samar da nono mai yawa da maiko me inganci ga mace mai shayarwa ita ce irin abincin da macen ke ci.


Yana da muhimmanci mace mai shayarwa ta rika shan ruwa mai tsafta da abinci mai ruwa-ruwa kamar Shayi da madara, kunu da sauransu kunun ma especially na gyeda Wanda aka hada shi a gida asaka masa gyeda yaji sosai.


Ga dai jerin abincin kamar haka: 


1- Hatsi 


Hatsi yana samar da ruwan nono ga mace Mai shayarwa sabida tana samarwa mata sinadaran bitamin E, B6 da B5 manganese, selenium da sauran su. Baya ga haɓaka samar da ruwan nono, yana intanta lafiyar garkuwar jikin yaro.


2- Alkama


Alkama wadda a turance ake kira Oatmeal tana da sinadarai masu gina jiki kuma ga saukin sarrafawa. Mai jego tana iya sarrafa alkama da madara ko da gyada domin kara dandano. Yana samar da ruwan nono sosai.


3- Alayyafo


Alayyafo yana daga cikin manyan manyan ganyw dake karawa uwa ruwan nono. Hakanan suna da wadata a cikin abubuwan antioxidant, wanda ke taimakawa tsawan lokacin shayarwa.


4- Shinkafa ta gida


Yana da kyau mai jego ta dena amfani da shinkafar da aka sarrafa ta a kasashen waje wanda muka fi sani da shinkafar gwamnati ta koma amfani da tamu shinkafar ta gida saboda ita ke dauke da sinadirai da take taimakawa wajen inganta ruwan nono.


5- Karas 


Idan mai jego na fama da karancin ruwan nono sai ta dage wajen cin karas ko kuma saka shi cikin abinci ko miyar. Karas na dauke da sinadarin vitaman A da wasu sinadaren da ke taimakawa wajen kara yawa da ingancin ruwan nono.


6- Tafarnuwa


Baya ga yana dauke da sinadarai masu amfani diyawa. A gefe guda, yana ƙara samar da nono da ma yana kare jariri daga abin mamakin ciki. Mace za ta iya ci haka ko anika shi a cikin abinci.


 7- Dankalin Hausa


Dankalin hausa yana dauke da sinadarin potassium da kuma carbohydrate da ke matukar taimakawa wajen kara inganci ruwan nono da kuma magance kasala. Ana iya dafa dankalin a ci da miya ko a sarrafa ta wata hanyar.


8- Nonon Tsaniya


Madarar shanu da daya daga cikin abincin da ke kara yawa da inganci nono ga mai jego. Baya na nonon sauran ababen da ake fitarwa daga nonon kamar kindirmo da man shanu ko Yoghurt duk suna taimakawa suma.


9- Kunu


Kunu yana daya daga cikin abincin iyaye da kakanni ke bawa mai jego ta sha da zarar ta fara shayar da jaririn da ta haifa musamman a kasar Hausa. 


Ana iya sarrafa shi da gero ko masara a bawa mai shayarwa.



Post a Comment

0 Comments