IDAN MIJINKI BAYA SADUWA DAKE GA SIRRIKAN DA ZAKIYI AMFANI DASU CIKIN SAUKI 'YARUWA
Akwai dubanni matan da suke gidajen aurensu suna zamane ba tare da mazan na Jima'i dasu.
Akwai matan da suke kokawa suce mazansu na daukan tsawon lokaci wasu har sama da shekara basu Kusance su ba. Wasu mazan ma idan sun tashi saduwan dasu basa cin zakara suke musu. Masu jimawan kuma suna yi domin gamsar da kansu ta hanyar sa mace ta musu abunda suke so amma su baza su iya yiwa matan nasu abunda suke so ba..
Tsakanin miji da mata mutum dake waje bazai iya yanke hukunci ba, amma idan har kin samu kanki cikin matan da mazansu basa saduwa dasu. To ga abunda ya kamata kiyi.
WOMEN HEALTHCARE
1: ABU na farko daya dace kiyi shine duban ta hanyar da kika zo gidan wannan mijin naki..
Akwai soyayya a tsakanin ku kamin kuka yi aure, ko dai kawai an cusa masa kece, idan har kina son shi yana sonki kuka yi wannan auren, to ki duba wasu irin halayene naki da kike masa waje da cikin Jima'i wanda baya so, da wannan ne zaki iya gano mataki na gaba.
2: Ki duba mijinki wani irin aiki yake yi, aikin da yake yi yana samun hutu yadda ya kamata ko dai lokacinda na kasancewa a wajen aiki yafi na hutawarsa yawa.
Duk Namijin da bai samun hutu sosai, sha'awar Jima'i fita yake daga jikinsa da ransa, idan kuma ya takurawa kansa sai yayi, ba zai iya gamsar da mace ba.
Don haka idan har mijinki mutum ne da yake cikin sugunla da rashin samun hutu, dole ne ki samu lokacinda ya huta kamin kine mi yin Jima'i da shi.
Wannan yasa nake baiwa masoya shawara kamin su amincewa juna, suyi la'akari da irin aiki ko sana'ar da suke gudanarwa domin zai shafi zamantakewarsu.
3: Namiji ko kazami ne bai son mace kazama. Ki tabbata kina gyara jikin ki yadda namiji yake son ganin matarsa. Kin tabbata gabanki, bakinki, hamatanki, matsaimatsinki, duburanki basa buga masa hanci da wari a duk lokacin daya kusance ki?
Ki kara duba yanayin tsaftar jikinki sosai domin tabbatar da cewa ba wannan bane yasa yake nisantarki ba.
4: Akwai mazan da sun saba da yin Istimina kamin suyi aure, idan har suka yi aure suka kasa samun dadin Jima'i daga wajen matarsu zasu ci gaba da yin Istimina ne, idan kuma sun yi ko suna yi, ba lalle bane yin Jima'i da matansu ya damesu ba. Wannan yana daya daga cikin illar Istimina idan ya kama mai yi.
Sai dai idan har kin tabbatar da hakan ke hanashi kusantar ki, sam kada ranki ya baci, nuna masa zaki iya masa wasan daya fi Istimina dadi, daga nan sai ki rika masa wasan janjage da shan buransa, ki daure koda bai saduwa dake a tsakanin wannan lokacin da kike masa wasan nan, muddin kika saba yi masa zai daina yin Istimina zai koma sawa kina masa daga nan kuma zai dawo yana saduwa dake. Amma sam kada ranki ya baci don kin gano mijinki na yin Istimina.
Sai dai idan har bayan kin gano hakan yaki amincewa da ki rika masa, to ina tabbatar miki mijinki yafi sha'awar maza ne akan mata, don haka koda zaki masa bazai gamsu ba kuma bazai daina ba.
5: Wasu mazan halayen matansu ke hanasu kusantar su a Jima'i.
Kina cikin matan da miji na shigowa gida za a fara bashi labarai marasa dadi. Ko kina cikin mata masu mita ko masifa.
Babu yadda mutum zai ji sha'awar Jima'i a lokacin da bai da kwanciyar hankali, koda kuwa zai yi bazai yi yadda ake bukata ba. Don haka idan mace ce mai matsala kike to kima daina kokawa akan rashin saduwa dake da mijinki baya yi, kece kika sa.
6: Ba duk wata gaskiya bace ake fadawa mutum ba. Akwai Matan da suke fitowa fili su sanarwa mazan da zasu auresu irin zinar da suka yi a baya, ciki ma kila da mutanen da mazan suka sani, ko kuma ma abokan su, wannan gaskiyan zai iya miki illa nan gaba.
Mace na iya ganin namijin datake so da wata turmi cikin tabarya, taci kukanta ta ci gaba da son namijin. Amma shi namijin ko yaci gaba da mu'amala dake wannan abun yana ransa.
Idan kin fadawa mijin da kike aure irin rayuwar zina da kika yi da wasu mazan, bayan auren ku zaki fice masa a rai. Ba ina zancen zai ci gaba da zargen ki bane koda bakiyi abun zargi ba, kawai zai rika rayawa a ransa tamkar ba gamsar dake yake ba, ko kuma da zaran wannan labarin ya fado masa a lokacin da ya tashi saduwa dake sai ya ji sha'awar sa ya kwanta.
Duk tsiya kada ki taba fadawa wanda zaki aura cewa kinyi zina da wasu har ma kina bashi labarin yadda kuka yi ko abunda kuka yi. Kai ko yasan kin taba haihu ba aure, kada ki bashi labarin zinar barshi akan kin taba haihuwa, yadda akayi kika yi cikin kuma wannan akwai hanyoyin yi da dama ciki har da fyade amma ba ki bashi labari ba.
7: Kin taba kuskuren furta wata kalma a lokacin da mijinki yake kanki?
Akwai wasu matan idan mazansu na cinsu sai su rika yin subutar baki, suna kiran sunan tsoffin mazansu, Samarinsu ko kawayensu na madudo.
Wasu kuma matan tsabar santin ci labaru marasa dadi zasu yi ta fitowa dasu sunanta fadawa mazan nasu a lokacin da ake saduwa dasu.
Idan har kina cikin irin wadannan matan, mijinki zai rika yin nesa dake a Jima'ice domin ma kada ki sakar masa labarin da zai bata masa rai.
8: Wasu matan kushe halitta da kokarin mazansu suke yi a lokacin da suke saduwa dasu ko kuma bayan sun gama.
Akwai macen da zata dubi buran mijinta ta kushe tace ko yayi kankanta, ko yayi girma ko kuma yana lankwashe.
Wasu kuma ana gaba Jima'i zasu nunawa namiji bai iya yin abu kaza da kaza ba. Muddin kina yiwa namiji haka to bazai rika sha'awar saduwa dake.
A duk yadda yake, a irin yanayin daya sadu dake nuna masa yayi kokari, sannu a hankali kina nuna masa yadda kike so yayi ko ya zama zai zama. Amma kada ki nemi cusa masa abunda kika koya ko kika saba a gidan wani ko kike kallon a finafinan batsa kice haka zai miki ko zai kasance, sam zai guje miki.
9: Kina cikin matan da suke kure mazajensu idan suna Jima'i dasu. Ko kina cikin matan da basa iya gamsar da mazansu. Muddin kika zama guda daga cikin irin wadannan matan, dole namiji ya gujeki.
Idan har kika matsawa mijinki da ci, idan kuka soma baki san a daina ba, zai rika gudun ki, idan kika zama wacce bata iya gamsar da mijinta ne daga an soma zata gamsu kuma tace ta gaji haka, zai rika gudun ki..
Idan har baki son mijinki ya rika gudun ki a irin wannan yanayin, dole ne ki sauko idan kina da karfin sha'awa, ko kuma ki haura idan kina da karancin sha'awa.
Ba lalle bane sai kun zama daidai ba, amma zaku iya ragewa juna zafi yadda baza a cutar da juna ba.
10:................. A naka tunanin maike sa namiji kauracewa matarsa wanda bamu kawo a wannan darasin ba???
0 Comments