CIWON MASASSARAR HANJI (TYPHOID FEVER) ABINDA KE KAWOSHI ALAMOMIN SA TARE DA HANYAR MAGANCEWA DA IRIN MAGUNGUNAN DA ZA'AYI AMFANI DASHI
Zazzabin masassarar hanji wanda akafi sani da "TAIFOT" larura ce da kwayar cutar bakteriya da ake kira "selmonela taifii" ke haddasa sa, yayin da wannan kwayar cutar ana daukarta ne ta hanyar ci ko shan gur6ataccen abun data shiga ciki ko ta hau kai, ko kuma ta hanyar mu'amala da mutum me dauke da kwayoyin cutar wato mai ciwon taifot din.
Ciwo ne mai hatsarin gaske dake kisa musamman a kananan yara yan kasa da shekara 5 da kuma manya... Shiyasa ciwone da duk wanda ya kama kwai bukatar a kauwamesa ahana mutane ra6arsa wato asashi a "isolation" kamar yadda akewa masu cutar corona,
Haka ma asibiti bai dace a hada mai typhoid da sauran marasa lfy ba, dakinsu daban ake warewa.
Saide bakowa ya kwan da sanin hakan ba. Yana da tsanani gamin da sa arasa rayuka.
𝐌𝐚𝐧𝐲𝐚𝐧 𝐚𝐥𝐚𝐦𝐮𝐧𝐬𝐚 𝐭𝐚𝐬𝐡𝐢𝐧 𝐟𝐚𝐫𝐤𝐨 𝐢𝐧𝐲𝐚 𝐤𝐚𝐦𝐚 𝐦𝐮𝐭𝐮𝐦 𝐬𝐮𝐧𝐞;
1- Zazzabi
2- Ciwon kai
3- Ciwon Ciki
4- Gudawa ko Atini wato taurin bayan gida arika nishi.
Ciwo ne wanda galiby yanzu kasashen da sukaci gaba aduniya babu shi sai kadan, yafi kamari akasashe masu tasowa musamman yankin africa da Asia.
𝐌𝐄𝐊𝐄 𝐇𝐀𝐃𝐃𝐀𝐒𝐀 𝐂𝐈𝐖𝐎𝐍
Kamar yadda nafada kwayar cuta ce ta bakteriya ke haddasa musamman ta hanyar shan gur6ataccen ruwan sha ko abinci data shiga ciki, ko ta hanyar wanke kashi ko fitsarin me dauke da ita inda shima batare da kyakkyawan wanke hannu ba yaje yana cin abinci da hannun ya dauki cutar. Ko kuma ta hanyar ra6ar jikin mai dauke da kwayar cutar agogi guminsa a hannu a manta ba awanke hannun aci wani abu, ko miyau dinsa, fitsarinsa ko jininsa... ko amfani da bandakin da yai fitsari ko bayan gida.
Yawanci mutane na kamuwa ne ahali na tafiya ko zaman cikin motar haya, ko kuma ta hanyar amfani da bandakuna a irin inda ake da gidajen wanka.
Koda bayan amfani da magani anji sauki ance mutum ya warke duk da haka kwai wadanda kwayoyin cutar na jikinsu wato babu alamun ciwon amma duk inda suka tsuguna sukai bayan gida ko fitsari toh duk wanda yazo gun ya tsuguna sai ya kamu wato sun zama "Chronic Carriers" shyasa kada mutum ya raina dan saken dazai yaga ya kamu da cuttuka. Typot ciwone dake iya yaduwa daga wani zuwa wani cikin sauki
Shyasa duk wanda yake ba mazauni ba bayan anmasa treatment din typhoid toh dama akwai rigakafinsa da ake ko ta digawa abaki wato "Vivotif vaccines" ko na allura wato "injectables" da ake musu, don kubutar da sauran mutane. Kai koda mazauni nema agida.
𝐂𝐈𝐊𝐀𝐊𝐊𝐔𝐍 𝐀𝐋𝐀𝐌𝐎𝐌𝐈𝐍 𝐂𝐈𝐖𝐎𝐍
Kamar yadda na lissafa alamu 4 manya asama haka suke, saide cikinsu bakowa ne ke haduwa da duk wadancan alamomi hudun ba... akwai karin wasu alamonin da dama dake bayyana ahankali a tsai-tsaye- a tsai-tsaye daga sati 1 da kamuwa da cutar zuwa sati na 3 aka sun bijiro sun kwantar da mutum kamar haka:
▪︎Zazzabi mai zafi da tempreture kan kai 40°C, ko kaga mutum atsai-tsaye a tsai-tsaye da safe zuwa rana lfy amma da yamma ta doso yaji zazza6i ya rufesa.
▪︎Kasala aji ba karfi ajika
▪︎Ciwon kai
▪︎Zufa wato yawan gumi
▪︎Ciwon ciki
▪︎Rashin son cin komi
▪︎Ramewa aga andan faffada
▪︎Kumburin ciki
▪︎Tari wanda ba'a fitar da komi
▪︎Gudawa ko Atini wato taurin bayan gida arika nishi.
■ In duk bayan wadancan alamomin mutum bai wani abu ba, ko kuwa baije ga likita ya sami cikakkiyar kulawa ta typhoid ba... yakan iya zamowa ya fara ficewa hayyacinsa, kwanciyama babu karfin yinta saide yake zirarewa atsaye ko aga yana tafiya daga-daga zai fadi kasa, yaji idanunsa sun rurrufewa wanda wannan shi muke kira "Delirious typhoid state"
A wannan hali illolin ciwon dake haddasa mutuwa ke fara bayyana, za a iya jin ansamu sauki amma bayan sati biyu alamomin zasuyo ribas daga nan kila kaji ance wane ya mutu... kila saide aita duba Bp da sauransu ana malaria ce alhalin typhoid ne,
Shyasa ko yaushe akeson ma'aikacin lafiya ya hada hankalinsa guri guda ya lakanci presentation na cutuka daban daban domin wasu na kamanceceniya da wasu basirarka ce zata taimaka ka rarrabe batare da kasa mara lafiya yawon kashe kudi yana yin Test- Tests marasa amfani ba
𝐓𝐀 𝐘𝐀 𝐊𝐖𝐀𝐘𝐀𝐑 𝐂𝐔𝐓𝐀𝐑 𝐊𝐄 𝐒𝐇𝐈𝐆𝐀 𝐉𝐈𝐊𝐀 𝐓𝐀𝐈 𝐈𝐋𝐋𝐀𝐇??
A yayin da wannan kwayar cuta tasamu damar shiga cikin mu ta hanyar gur6ataccen abinci ko abun shan mu ko wanda muka ta6a da gurbataccen hannun mu tana zarcewa zuwa uwar hanji wato stomach, stomach dinnan nan ne inda peptic ulcer ke faruwa kuma anan abincin d. Muka ci ke fara dahuwa... gurine mai tsananin zafi saboda acida, da zaka jefa Reza narkewa zatai amma wannan kwayar ta salmonella tana da juriyar wannan yananyin.
Daga uwar hanjin zatabi karamin hanji tai kasa har saitaje mahadar inda karamin hanji ya qare wato inda babban hanjiya fara.. to anan ne zata tare tafara kyakyansa tsawon kwana 21 daga nan ne alamun ciwon ke fara bayyana, su kuma sojojin jiki macrophages jin alamun jiki ba lafiya zasu zo su hadiyeta zuwa lymphatic system wato don karta cutar da jikinka....
Toh amma sakamakon baka sha magani ba in sun kamo kwayar cutar sai karshe kwayar cutar tafi karfinsu wato sun kamo abunda yafi karfinsu.. don haka daga mesentric lymphatic na hanjin inda suka jata suka kai.. saita danna ta cikin butuntun lymph din tai sama zuwa hanta, 6argo, da saifa, daga nan cikakkun alamun ciwon da kukaji na ambata asama ke qara bayyana.
Toh ana hakane inta ru6anya tai yawa saita fi karfin kwanson da take ahantar don haka kunga kwanson zai fashe kenan to da ya fashewa tsokar gefe zata mutu tunda ba jini, toh fashewar tsokar bayan mutu shi zai bude kofar da kwayar cutar daga hanta zata sami damar shiga bile duct wato hanyar ruwan matsalmama gallbladder daga nan ne zata samu kofar shiga jijiyar jini.....
Kunga jini koh ba inda inka fasa ajika bazaka gansa ba don haka kai tsaye zata karade ko ina ajika daga nan ne komi kan iya faruwa ba alamar da bazaka gani ba, inba adau mataki ba shine complications wato illolin ciwon da zakuji akasa zasu soma faruwa sukai ga mutum ya mutu in ba ai dace ba.
𝐖𝐀𝐊𝐄 𝐂𝐈𝐊𝐈𝐍 𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐑𝐈𝐍 𝐊𝐀𝐌𝐔𝐖𝐀 ???
Duk shekara akalla mutum milyan 27 ke kamuwa da typhoid. Masu hatsarin kamuwa sun hada da:
■ Kasancewarka bakar fata dan Africa ma hatsari ne, domin yankine da cutar tai kamari bakasan a inda zaka ci karo da ita ba.
■ Idan wani dan gida ya kamu da typhoid kuma sauran kuna cikin hatsari
■ Kasancewa shadda ko bandakin gida na kowa da kowa ne
■ Rashin ingantaccen ruwan sha ko nayin girki shima hatsari ne
■ Sai kasancewa maikacin lafiya musamman bangaren gwaje-gwaje laboratory shima kwai hatsarin kamuwa.
𝐈𝐋𝐋𝐎𝐋𝐈𝐍 𝐂𝐔𝐓𝐀𝐑 𝐓𝐘𝐏𝐇𝐎𝐈𝐃
Idan ba adau matakin da ya dace ba, typhoid na iya kaiwa ga haddasa:
1. Ɓulewar hanji wato perforation, wanda in dattin kashi ya zuba zuwa ga sauran kayan ciki awa 5 da faruwar hakan ya isa ya kashe mutum murus, domin kai tsaye zaiji ya fara fuskantar tashin zuciya, kuraje, amai, murdawar ciki da sa kwayoyin cuta su shiga jijiyoyin jini.
Kunga kenan wadannan alamomin na kuraje, amai, tashin zuciya da matsannancin ciwon ciki basu daga cikin wanda na lissafa asama alamace ta inkana da typhoid ka fara jin amai da tashin zuciya da murdewar ciki toh kaji tsoron abunda ka iya biyo baya.
2. Yana iya ta6a naman zuciya yai masa rauni abunda ake kira Myocarditis... Haka yana iya ta6a mayanin cikin zuciyar wato endocarditis koma amurfin aljifan zuciya wato valves inda hakan barazan ne ga rayuwa.🥲 Cikin kankanin kwanaki sai zance ya lalace
3. Ciwon sarkewar numfashi wato pneumonia, shyasa inkana da typhoid kaji numfashi ya fara maka nauyi toh kaji tsoron abun, ka fara developing complications.
4. Yana iya ta6a pancreas, wato abar dake saisaita suga ajika ta sanya pancreatitis... kaga intaci gaba da faruwa kana iya wayar gari da ciwon suga. Shine wani zakaji yace likita ji nai inda kasan ansa abu ta bayana anrarikeni anmun rami a baya haka naji azababben ciwo. Kwai yiwuwar pancrea ta ta6u
5. Yana iya sanya infection a koda da kuma mafitsara...
6. Sai kuma alamun juyewar kai; wato sumbatun surutai, ko mutum ya rika cewa yana ganin guri na juyawa, ko arika musu ana rigima dashi akan abunda ba haka yake ba.
𝐓𝐀𝐘𝐀 𝐀𝐊𝐄 𝐆𝐀𝐍𝐄 𝐀𝐍𝐀 𝐃𝐀𝐔𝐊𝐄 𝐃𝐀 𝐂𝐈𝐖𝐎𝐍
Likita na iya fahimtar alamun ciwon daga bayanan mara lafiya, sannan inya hararo typhoid din ne kai tsaye akwai gwajin jini da yaka iya nema mutum yayi, wanda zai nuna ana dauke da kwayoyin cutar ko babu.
𝐌𝐀𝐆𝐀𝐍𝐂𝐄 𝐂𝐈𝐖𝐎𝐍
Tunda kwayar cutar bakteriya ce ana baiwa mutum antibiotics walau magani ko allurai na tsawon kwanaki 14 ko 21, ya danganta da yadda mai larurar yai saurin responding amma de maganin baya gaza sati 2.
Galibi inda ake samun matsala kenan da anba mutum magani kwana 3 zuwa 5 anaga alamun ciwo sun tafu sai ai zaton ai ya warke alhalin ciwon na nan kurum remission ya shiga. Shayasa wasu ke ganin kamar ba a warkewa, a'ah treatment dinne ba ai na adadin kwanakin dazai kawo karshen ciwon ba. Lallai a tabbata anyi sati 2 koda anji babu alamun ciwon,
Kamar yadda nafada don ka dena jin alamun still kana iya cutar da wasu kana zuwa kai fitsari ko kashi wani ya dangwala shikenan, shima inyaje sai ya yadawa matansa.
Baya ga magance kwayoyin typhoid din kuma likita zai duba sauran matsalolin da ciwon ya haddasa; in akwai alamun karancin ruwa abaka ors ko akaramaka ruwa
Wanda bai iya cin abinci a bashi vitamins, wanda jikinsa babu kuzari abashi irinsu GLUCOSE D, in kuma hade da malaria ne itama ai maganinta, saide galibi maganin malaria kwana 3 akan warketa saide in kwayar cutar ba guda daya bace, tunda akalla kwayoyin malaria sunkai 5 wato falciparum, vivax, ovale, malarie, ko knowlesi. Shyasa itama zakaji ana batajin magani amma ankasa tunanin kila ba falciparum bace.. tunda yawanci treatment din da ake ba mutane na falciparum ne. Shyasa sai aga kamar resistance ne alhalin kwayar cuta daban maganin da ake yi daban
𝐌𝐀𝐓𝐀𝐊𝐀𝐍 𝐊𝐀𝐑𝐈𝐘𝐀
● Babban matakin katiya shine allurar rigakfi, akwai rigakafin typhoid da ake iya yi asamu garkuwa dagashi shikenan.
● Matasa masu zuwa bayan gari sui kashi wato open defecation wannan shine babbar hanyar da typhoid kan yadu ya nitsa yazo ga ruwan shan mu, dole ne ku fahimci illar hakan musamman a inda yake kusa da ruwa ko inda ake yin bulo irin na kasa domin yin gini. saboda da irin wannan ruwa ake kwa6a kasa tabbas ana iya debo kwayoyin cutar azo gida dasu.
Don haka aguji kashin nan abayan gari, inya kama dole to gara ahaka rami in anyi angama sai abinne.
● Tabbatar da tsaftar ruwan sha, ake wanke inda za'a tarasa, sannan in ana kokonton tsaftarsa asaka alif inya kwanta atace atafasa sannan ai amfani dashi
● Kula tsaftar bandakuna ta hanyar kada ruwan gishiri da omo ana wankeshi, da kuma muma kafin mushiga da bayan mun fito mu rika wanke hannuwan mu dakyau. Kamar yadda yanzu dinnan ake yawanyi ko mutsuka sanitizer saboda corona
● Kamar yadda nace ma'aikatan lafiya akoyi aiki da safar hannu ta asibiti wato gloves ko wanne department kake aiki wajibinka ne, saboda waniara lafiyar bakasan me ya ta6o ba. Sannan gloves din nan in akwai a wadace akalla duk bayan duba mutum 5 toh ka cire ka canza wata. In kuma akwai sanitizer toh duk mara lafiya daya ka fesa ajikin gloves din ka mutsuke hannuwan.
● Arika wanke kayan lambu da lyau kafin aci ko azuba a girki, musamman wanda ake iya ci danyu irinsu kankana🍉, ayaba,🍌 apple🍎, lemo🍋, kabeji, salad🥬 cucumber 🥒 da sauransu alura sosai da tsaftarsu ko don gudun kwalara.
● Arika dumama kwanannen abinci ko wanda ya riga ya jima yai sanyi kafin aci hakan zai taimaka
● Alura da tsaftar muhalli, data makarantu musamman nursery, da primary baki daya, shara da bude magudanan ruwa. inda hali aima rijiya murfi.
● Sannan ga masu cin abinci a waje mutum ya lura da tsaftar wajen mai saida abinci, komi tsadar abinci inda tsafta bamai tsada bane, haka komi arhar abinci inba tsafta mai tsada ne.
● In anji alamun ciwo kada azauna arika shan magani daka atafi ga likita
0 Comments