YADDA AKEYIN CABBAGE SOURCE NA ZAMANI ME DADIN GASKE
Abubuwan hadawa (INGREDIENT)
Cabbage
Green pepper
Peas
Green beans
Tarugu Tattasai
Seasoning
Gishiri
Man gyada
YADDA AKE HADAWA
Farko za ki yi grating tarugu da tattasai da albasa ki yanka lawashi ki ajiye gefe. Ki yanka cabbage da green pepper su ma ki ajiye su gefe. Ki zuba man gyada a tukunya, idan ya yi zafi, sai ki zuba albasa ki juya. Ki zuba grated tarugu da tattasai dinki ki na juyawa. Za ki dan rufe na mintina biyu sai ki wanke veggies ki zub, amma ba da cabbage da albasa ba sune karshe. Ki juya ki sa seasoning ki sake rufewa. Za ki bude idan ya dahu, sai ki zuba cabbage da albasa. Ba a so cabbage din ya dafe sosai dan haka minti biyu sai ki sauke. Shima wannan sauce ana ci da abubuwa da yawa tun daga farar shinkafa, da chappati, phateera, har ma su jellof rice.
0 Comments