YADDA ZAKUYI MAGANIN TUSAR GABAN MACE ( BUDURWA KO MATAR AURE )
Me Ke Janyo Tusar Gaba?
Yan Uwana Mata barkan mu da sake saduwa daku a cikin wannan shiri namu mai matukar farin jini, Wato Sirrin Iyayen Giji..
🌿
Kamar yadda ku ka sani shi wannan shiri a na yin shi ne don matan aure zalla domin ba su shawarwari ta ko wane bangare na rayuwarsu ta yadda za su samu su gyara zamantakewarsu da mazajen su da Mu’amalar su ta auratayya da ta bangaren girki, tsafta, gyaran gida da gyaran jiki da ma ko wane bangare da ya shafi rayuwar ’ya mace, da fatan ku na amfani da abubuwan da ake gaya muku. Ga cigaba da amsar tambayoyinku:
🌿
Assalamu Alaikum. Tambayata a nan ita ce, me ke kawo fitar iska daga gaban mace, wacce na ji wasu su na ce mata tusar gaba?
Dalilan Da Suke Kawo Tusar Gaba:
■🌿 Zama a kasa cikin na’urar AC ba wando kuma a kan tiles.
■🌿 Yawo ba takalmi, musammam a AC kuma kan tiles.
■🌿 Kwanciya ki kunna fanka kuma ba wando a jikinki.
■🌿 Rashin yin tsarki da ruwan zafi.
■🌿 Rashin yin tsarki bayan gama jima’I, wato barin maniyyi ya kwana a jikinki ba tare da yin tsarki ba.
■🌿 Yawan yin maganin mata ba gaira ba dalili.
■🌿 Cushe-cushen kayan matsi na mata barkatai. Ba ki san da me aka yi maganin ba kawai ki kama cusawa cikin gabanki.
■🌿 Matsanancin ciwon sanyi (infection), sai kaga ya cinye mace ta ciki ba tare da ta farga ba.
■🌿 Rashin iya ‘positioning’ na kwanciyar aure da miji.
■🌿 Zama da kamfai guda daya tun daga safe har dare. Sai ka ga mace ta bar shi tun safe har dare ya na jikinta tsabar kazanta.
■🌿 Rashin daure zani da karfi a ciki ga matan da suka haihu.
■🌿 Barin ciki da yunwa a lokacin da a ke al’ada ko lokacin da a ke Jego.
Wadannan kadan daga cikin Manyan abubuwan da ke kawo wa mata matsalar lalacewar gaba har ka ji yana ta kara yana fitar da iska Fut! Fut! Fut! kamar tusa.
Hanyar Magance Wannan Matsalar Ita Ce:
Ki nemi ganyen Magarya da Gabaruwa, da ’ya’yan Hulba.Sai ki hada su gu daya ki na dafawa sai ki tace kisa gishiri sai ki rinka shiga ciki 30min.
By Chef_Oum_Aslam✍🏻✍🏻
Masu Bukatar siyan Magungunan Mu kuyi Magana Muna Aika kayanmu kowane gari Munada Original Magungunan Mata Dana Gyaran Breast Hips Karin kiba Bridal sabaya package da sabaya 3IN1 da maganin sanyi sadidan dana dahuwar kaza dana ciccibi dana yanshila da tsumi gumba Zuma tabaje dana Rage Tumbi da kiba duk available kaduna state Nation wide delivery (07062950801).


0 Comments