KUSKUREN DA IYAYE KE TAFKAWA WAJEN TARBIYYAN 'YAYANSU A KASAR HAUSA
1. Rashin shayar da yaro nono yadda ya kamata: Wasu mata suna daina ba yaron nono da wuri ba tare da ya kai akalla watanni shida ba. Wasu kuma suna saurin haɗa nono da abinci da wuri sosai ga yaro, wanda zai iya kawo matsalar rashin lafiya ko ciwon ciki ga yaro. Rashin tsaftar nono ko kayan da ake amfani da su wajen shayarwa.
2. Ganin namiji ya fi mace daraja: A wasu gidaje, ana fifita tarbiyyar ’ya’ya maza fiye da mata, wanda ke sa ’ya’ya mata su ji basu da kima don ba a basu muhimmanci. Wannan yana iya haifar da rashin ƙarfin guiwa ga ’ya’ya mata tun suna ƙanana.
3. Tsananin tsoro da duka dukan yaro wajen gyara tarbiyya: Wasu iyaye suna amfani da duka da tsangwama sosai wajen tarbiyya, suna zaton hakan shi ne “horarwa”. Wannan yana iya sanya yaron jin tsoro ko ƙin bayyana matsalolinsa ga iyaye wanda saba musu fa dukan ke kara kangarar da su na rashin jin magana.
4. Rashin tattaunawa da yara: Matan Hausawa da dama ba sa yawan tattaunawa da yara game da abubuwan da suka shafi rayuwa ko tarbiyyar addini da zamantakewa. Yara suna buƙatar karin bayani da shawarwari don su samu fahimta mai kyau game da al'ada da abubuwan da suka shafi addini, musamman ta hanayr basu labarai da wakokin hikima da suka dace da addini da al'adun alummarsu.
5. Kauracewa koyar da ’yara sana’o’i da aiki: Wasu mata ba sa koya wa yara sana’a ko ayyukan gida tun da wuri, suna barin su suna zama ba aikin komai. Wannan na iya kawo gaggawar samun yaro mai rashin kwarewa ko rashin jajircewa kan ayyuka da neman halaliya.
6. Yawan dogaro da al’ada ba tare da tantance ta ba: Wasu tarbiyyar al’ada suna da kyau, amma wasu suna buƙatar a gyara su daidai da zamani da addini. Misali, hana yarinya neman ilimi saboda “zata yi aure” ba daidai bane.
7. Yawan sa yara cikin aikin gida fiye da kima:
Yara musamman mata suna samun nauyin ayyukan gida sosai fiye da damar da za su samu na karatu da hutu domin gina gobensu.
ALLAH ya bamu ikon gyarawa, ya bamu ikon sauke nauyin tarbiyyar yaranmu, yasa su cece mu gobe kiyama, Ammeen Summa Ameen.
Masu Bukatar siyan Magungunan Mu kuyi Magana Muna Aika kayanmu kowane gari Munada Original Magungunan Mata Dana Gyaran Breast Hips Karin kiba Bridal sabaya package da sabaya 3IN1 da maganin sanyi sadidan dana dahuwar kaza dana ciccibi dana yanshila da tsumi gumba Zuma tabaje dana Rage Tumbi da kiba duk available kaduna state Nation wide delivery (07062950801)


0 Comments