ABUBUWA GOMA (10) DA MAI CIKI YAKAMATA TA KULA DASHI MAI MATUKAR MUHIMMANCI
1. Ki runka yawan samun hutu,ki rage yin aikin karfi,ki runƙa hutawa sosai musamman a watannin ukun karshe na ciki.
2. Ki fara zuwa awo da wuri sannan ki tabbata kinje akalla sau takwas kafin kihaihu.
3. Ki yawaita cin abinci da shan ruwa,musamman idan kina jin ƙishi
4. Ki guji shan coffee(nescafe),ko ruwan lipton,kiyi nesa da su
5. Ki fara shan folic acid da sinadarin ‘iron’ tun daga farkon ciki har zuwa wata uku bayan haihuwa,
Lokaci mafi kyau daza ki sha wannan magunguna shine lokacin da za ki ci abinci.
6. Ki runka amfani da gishiri(iodized salt) a abincinki,hakan zai taimakawa jaririn dake cikin cikinki wajen kare shi daga matsaloli na rashin girma da wasu matsalolin bayan kin haifeshi,kuma kema zai kareki daga kamuwa da ‘ciwon goitre’
7. Ki tabbata kin fara shan sinadarin vitamin A dazarar kin haihu ko kafin kiwuce sati 6 bayan haihuwa,hakan zai taimakawa ɗan da kika haifa wajen samun isasshen wannan sinadari cikin nononki dakike shayar dashi.
8. Ki tabbata kin kare kanki daga zazzabin cizon sauro ta hanyar shan magungunan zazzabin sauro da ake bayarwa lokacin awo,bayan nan ki runka bacci cikin gidan sauro.
9. Ki yawaita kula da tsaftar jikinki da da abin da kike ci.
10. Ki yawaita duba nauyin jikinki,anaso akalla nauyin jikin ki ya runka ƙaruwa da kilo daya duk wata.zamuyi cikakken bayani akan wannan a rubutun mu na gaba.
Ciki da raino by Chef Oum Aslam✍️
Kuyi sharing domin yanuwa su amfana


0 Comments