Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

NA AURETA A MATSAYIN BUDURWA AMMA TUN A DAREN FARKO NA GANE CEWA BA BUDURWA NA AURABA


NA AURETA A MATSAYIN BUDURWA AMMA TUN A DAREN FARKO NA GANE CEWA BA BUDURWA NA AURABA



Ba sai mace tayi mu'amala da wani take samun wanan matsalar ba. 

Wata yakan zama fyade tun tana yarinya, wata kuma a irin iyayin su na neman gira ake rasa ido,  ma'ana garin jarabar gyara da iyaye ke musu na shiga ruwan zafi tsarki da ruwan zafi me zafi so sai wai sabida kore sanyi, wata kuma yawan daukar abu me nauyi, wasu hawan keke, da tsalle tsalle, wasu kuma garin kini bibin cusa maganin sanyi da hannu sanan a wanko shi da yatsa loko da sako sai kace ta sami tukunyar dafa abinci. 

Sanan ga yanayin abinci da muke ci bafa irin na da bane. 

Sanan wata ko ta kirjinta za'a fahimci tana mu'amala ta banza. 

Ba kare ta nayi ba dan tana yar uwata mace, nadai kawo dalilan da sukan sa a rasa wanan fatan. 

Toko a yawan rawa da karkada kugu da tsalle abinkin kauyawa dai ai za'ana samin matsa. 

Lalacewar mata yanzu takai inda mutum kamar yayi kuka! Sabida an shiga rayuwar da wai uwace zatace yar ta bani aron dubu guda, dan cika mana muyi cefane! 

A gidan ubanwa zat samu tunda ke da ubanta ba bata kuke ba, kunbar ma samari duk wata larurar ta datake kanku! 

Yanzu Allah ya kawomu zamanin kwadayi da buri na sai mace ta mallaki babbar waya, ankon duniya na kawaye baya wuce ta! 

Idan ba iyaye bane ke mata tsinta take a bola? Shi wanda zai batan murmushi kawai zatai ya bata? 

Mata suna rasa kimar sune sabida takamar ai ana saida madadin sa a kasuwa! To wallahi karya masu maganin mata suke, wanan darajar in ta tafi ta tafi kenan. 

Matukar baka taba zina Allah zai baka mace saliha wace ta tsare mutuncin ta. 

Idan ka sami mace wacce bata kama kanta ba fara tuhumar kanka! 

Amma akwai wanda Allah yake jarabtar su da wacce take ballagaza, haka itama macen Allah yana jarabtar ta da wanda bashi da aiki sai bin mata. 

Allah ya shiryar damu.



Post a Comment

0 Comments