Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

KIN TAƁA TAMBAYAR KANKI ME YAWAN FADA DA MIJI ZAI IYA HAIFARWA KUWA?

KIN TAƁA TAMBAYAR KANKI ME YAWAN FADA DA MIJI ZAI IYA HAIFARWA KUWA?


Wani lokaci mace da miji suna yin sabani, sai ka ji ana cewa: “Ai fada ne kawai, gobe za mu sulhunta.” 😅

Amma ki kula… ba duk wani fada ne yake wucewa ba tare da ya bar wani abu a zuciya ba.

Idan sabani ya zama kullum, kalamai masu zafi suka zama ruwan dare, kuma kowace karamar magana tana iya zama dalilin tashin hankali, a hankali soyayya na iya fara rasa natsuwarta.

Miji ya fara jin tsoron yin magana saboda duk abin da zai fada zai iya zama “case” 😂.

Mace kuma ta fara jin kamar mijinta baya fahimtarta.

Daga nan sai abin da ya fara a matsayin ƙaramin sabani ya koma nisantar juna, rashin magana, rashin kulawa da kuma sanyin zuciya.

Amma wannan ba yana nufin kada ki taɓa yin fushi ba.

Fushi ba laifi ba ne. Yadda kika sarrafa fushin ne yake da muhimmanci.

Idan kina cikin fushi, ki koyi yin shiru na ɗan lokaci maimakon ki furta kalmar da za ki yi nadama a kanta bayan kin huce.

Kada ki yi amfani da sirrin mijinki wajen cutar da shi lokacin fada.

Kada ki zagi iyayensa.

Kada ki kawo tsohon kuskure goma domin kawai kina son ki “lashe” wannan sabon rigimar. 😂

Aure ba gasar cin kofin duniya ba ce da sai an samu wanda ya ci da wanda ya sha kashi.

Aure haɗin gwiwa ne.

Wani lokaci cin nasara a cikin gardama na iya zama rashin nasara ga auren gaba ɗaya.

Ki tambayi kanki:

“Abin da nake shirin fada yanzu zai gyara matsalar ne, ko zai ƙara girman ta?”

Idan zai ƙara girman ta, ki dakata.

Ki huce.

Sai ku tattauna cikin nutsuwa.

Domin mace mai hikima ba wai wadda ba ta taɓa yin fushi ba ce; mace mai hikima ita ce wadda ta san lokacin da za ta yi magana, da lokacin da ya kamata ta yi shiru.

Kuma ku maza, kada ku manta… 😄

Idan matarka ta yi shiru ba lallai yana nufin komai ya yi kyau ba. Wani lokaci shiru yana nufin: “Na gaji da yin bayani.”

Saboda haka, ku duka biyun ku koyi sauraron juna.

Auren da babu sabani babu, amma auren da ma'aurata suka koyi yadda za su warware sabani cikin mutunci shi ne yake samun damar dorewa. ❤️

👉 Ke fa, idan kika yi fushi da mijinki, kina fi son ki yi shiru ne ko ki yi magana nan take?
Masu Bukatar siyan Magungunan Mu kuyi Magana Muna Aika kayanmu kowane gari Munada Original Magungunan Mata Dana Gyaran Breast Hips Karin kiba Bridal sabaya package da sabaya 3IN1 da maganin sanyi sadidan dana dahuwar kaza dana ciccibi dana yanshila da tsumi gumba Zuma tabaje dana Rage Tumbi da kiba duk available kaduna state Nation wide delivery (07062950801).



Post a Comment

0 Comments