Ticker

6/recent/ticker-posts

Header Ads Widget

Responsive Advertisement

DALILAN DA YAKE JAWO CIWON HAƘORA DA KUMA YADDA ZAKU MAGANCE MATALAR FISABILILLAH

DALILAN DA YAKE JAWO CIWON HAƘORA DA KUMA YADDA ZAKU MAGANCE MATALAR FISABILILLAH.


Wannan tambaya ce da Mutane da yawa suke yi, Sai dai amsar bata musu daɗi, cewa 'RASHIN INGANTACCIYAR TSAFTAR BAKI' mutum Sai ya ga kamar ka raina shi ne kana nufin baya goge Baki.


Yau zamu tattauna akan menene rashin ingantaccen tsaftar baki ( Poor Oral Hygiene ).


Rashin ingantacciyar tsaftar Baki yana nufin ƙarancin kula da Baki wanda ya kunshi Haƙora, Dadashi, Harshe da sauran halittun dake Baki, wanda yake sanadiyyar ciwon Haƙora ko wani sassa daga cikin Bakin.


Rashin ingantacciyar tsaftar Baki ya haɗa da:


1. RASHIN GOGE BAKI: ya kasance mutum baya goge Bakinsa kwata-kwata ko baya gogewa sau biyu a rana wato bayan karin kumallo da kuma lokacin kwanciya bacci, idan mutum zai goge baki sau biyar a rana amma babu waɗannan lokutan ciki to bashi da ingantacciyar tsaftar Baki, haka kuma idan mutum baya amfani da 'Brush' ɗin da ya kamata ya goge Baki da shi ( Medium toothbrush ) to koda yana goge Bakin cikin lokutan can bashi da ingantacciyar tsaftar Baki.

Haka nan akwai hanyar da ake bi wajen goge Bakin ( ideal brushing techniques) ita ma idan ka saɓa da wannan hanyar, koda kana gogewa sau biyu a lokacin da ya dace kuma da Brush ɗin da ya dace to baka da ingantacciyar tsaftar Baki.


2. RASHIN SAKACE TSAKANIN HAƘORA: Idan mutum baya sakace tsakanin Haƙora sau ɗaya a kullum to koda yana Goge Bakin akan ƙa'ida bashi da ingantacciyar tsaftar Baki. Saboda Brush baya shiga tsakanin Haƙora ya fitar da Dattin gaba ɗaya.


3. ƘARANCIN AMFANI DA SINADARIN 'FLUORIDE':  Rashin amfani da makilin mai ɗauke da sinadarin 'Fluoride' ko Ruwan sha  mai ɗauke da sinadarin 'Fluoride' yana nufin baka da ingantacciyar tsaftar baki koda kana goge Baki sau biyu a yini.


4. SHAN KAYAN ZAƘI: Idan mutum yana Shan abubuwan zaƙi sosai ko Acids to bashi da ingantacciyar tsaftar Baki.


5. ƘARANCIN KUSKURAN BAKI: Ana so mutum ya yawaita kuskure Bakinsa haka nan, da kuma a duk lokacin da ya ci wani abu musamman mai zaƙi, akasin haka yana nufin baka da ingantacciyar tsaftar baki kuma kana iya kamuwa da ciwon Haƙora.


6. RASHIN ZIYARAR ASIBITI SAU BIYU A SHEKARA: Ana son kowanne mutum ya ziyarci asibitin Haƙora aƙalla sau biyu a shekara ( duk bayan wata shida ) wannan yana nufin ko bakajin wata matsala a Bakin naka matukar kana fatan zama da Haƙoranka lafiya. Acikin wannan ziyarar akan yi wa mutum wankin Baki ( Scaling and polishing ), Hanya ce da take taimakawa sosai wajen kiyaye lafiyar Baki saboda Brush baya cire kowanne Datti. Idan kana kiyaye abubuwan da aka lissafa sama amma baka ziyarartar asibiti to baka da ingantacciyar tsaftar Baki.


Yawancin cututtukan Baki suna faruwa ne saboda rashin ingantaccen tsaftar Baki.


Rashin ingantaccen tsaftar Baki yana jawo cututtukan Baki irin su :

1. Kogon Haƙori ( Dental caries/dacay/ Cavities)

2. Ciwon Dadashi ( Gum diseases)

3. Warin Baki ( Bad breath / Halitosis)

4. Da sauransu.

Kula da Tsaftar Baki yana tabbatar da kariya daga cututtukan Baki.

Allah ya datar da mu Ameen.

Masu Bukatar siyan Magungunan Mu kuyi Magana Muna Aika kayanmu kowane gari Munada Original Magungunan Mata Dana Gyaran Breast Hips Karin kiba Bridal sabaya package da sabaya 3IN1 da maganin sanyi sadidan dana dahuwar kaza dana ciccibi dana yanshila da tsumi gumba Zuma tabaje dana Rage Tumbi da kiba duk available kaduna state Nation wide delivery (07062950801)




Post a Comment

0 Comments