KADA KA TABA FADA WA MATARKA WADANNAN KALMOMIN KO DA KUNA CIKIN TSAKIYAR FADA NE
Gaskiya tana da daci, amma dole mu sha ta don mu warke.
Akwai wani Sirrin Zaman Lafiya da wani Tsoho mai hikima ya taba bayarwa, wanda maza da yawa suke mantawa da shi a lokacin bacin rai.
Ya ce:
"Kada ka taba fadin kalmar da za ta rusa yardar matarka, ko da kuwa kana cikin kololuwar fushi."
Maza da yawa suna dauka cewa nuna karfi a wajen fada shine mazantaka.
Amma sun manta cewa kalma daya tak, tana iya rushe ginin shekara goma.
GA KUSKUREN DA MAZA KE YAWAN YI
1. KALMAR IDAN KIN GA DAMA, KOFA A BUDE TAKE:
A lokacin da kuka samu sabani, sai ka ce mata: "Idan kin ga dama ki tafi gidan ubanki." ko "Na gaji da ke, ki kama gabanki."
A take, za ka ga ta yi Shiru.
Ba wai ranta ya baci bane kawai... Zuciyarta ce ta Karye.
Me yasa?
Saboda har zuwa wannan lokacin, tana ganin cewa Gidanka shine Gidanta. Tana ganin nan ne Wajen Tsaronta.
Amma wadannan kalmomin sun nuna mata cewa: Ashe ba Gidana bane, Haya nake yi. Duk lokacin da na yi laifi, za a iya kore ni.
2. DAGA AMANA ZUWA TSORO:
Daga ranar da ka yi mata barazanar saki ko korar ta...
Ko kun shirya, ko kun yi Hug, ko kun ci abinci tare...
Akwai wani abu da ya mutu a zuciyarta.
Ba za ta sake sakin jiki 100% ba.
Za ta fara rayuwa a cikin Tsoro, tana tsoron yin magana, tana tsoron yin kuskure, saboda tana ganin kamar tana zaune ne akan Bama-bamai.
Gidan da ake tsoron korar mutum, ba Gida bane, sansani ne.
3. NASARA A FADA, ASARA CE A SOYAYYA:
Hikimar Tsohon nan ta kara da cewa:
"Kada ka zama Namijin da yake son ya yi Win Argument... Ka zama Namijin da Matarsa take iya yin kuka a gabansa ba tare da tsoron cewa zai wulakanta ta ba."
Dan uwa,
Mata suna iya yafe komai, amma suna dadewa basu manta Wulakancin da aka yi musu lokacin da suke bukatar rarrashi ba.
Idan kana son gidanka ya dore...
Ka hadiye fushinka.
Ka sa ta ji cewa ko duniya ta ki ta, kai kana nan tare da ita, kuma Gidanka Gidanta ne har abada.
ALLAH KA TSARE HARSHENMU DAGA FURTA ABINDA BAI KAMATA BA


0 Comments