MATAKAN DA ZAKI BI WAJEN MAGANCE CIWON MARA LOKACIN AL'ADA WATO (MENSTRUATION) A GIDA
HANYOYIN MAGANCE CIWON AL’ADA A GIDA
Ciwon al’ada (dysmenorrhea) matsala ce da mata da dama ke fuskanta, kuma yawanci ana iya rage shi ta hanyoyin gida idan ba ya da tsanani. Waɗannan hanyoyi suna taimakawa wajen sassauta tsokoki na mahaifa, rage zafi, da ƙara jin daɗi ba tare da amfani da magani mai ƙarfi ba.
• GASHIN MARA DA RUWAN ƊUMI (WARM HEAT THERAPY)
Sanya ruwan ɗumi a gorar ruwa ko jiƙa tsumma da ruwan ɗumi a ɗora a kan mara ko baya na taimakawa wajen sassauta tsokoki da rage zafi. Zafi yana ƙara gudun jini a wajen, wanda hakan ke taimakawa rage ciwon al’ada.
SHAN RUWAN ƊUMI DA KUMA SHAYI
Shan ruwa mai ɗumi da shayi mai ɗauke da ginger, ko mint na iya rage kumburi da zafi. Ginger musamman yana da sinadaran da ke rage ciwo da amai.
MOTSA JIKI MAI SAUƘI
Motsa jiki mai sauƙi kamar tafiya, ko yoga na taimakawa wajen sakin sinadaran farin ciki (endorphins) a jiki, wanda ke rage jin zafi da damuwa.
KULA DA ABINCI
Cin abinci mai sauƙin narkewa, rage mai da yaji, da ƙara cin kayan lambu, ’ya’yan itatuwa, da abinci mai ɗauke da iron da magnesium na taimakawa wajen rage ciwon al’ada.
HUTU DA BACCI
Samun isasshen bacci da hutawa na taimakawa jiki ya murmure, tare da rage gajiya da zafin al’ada. Kwanciya a matsayi mai dacewa na iya sauƙaƙa ciwon.
TAUSA (GENTLE MASSAGE)
Tausar mara ko baya da man rage ciwo (kamar man zaitun) na taimakawa wajen sassauta tsokoki da rage ciwo.
A TAKAICE:
Hanyoyin gida na iya taimakawa sosai wajen rage ciwon al’ada, amma idan ciwon ya yi tsanani, ya daɗe, ko yana tare da zubar jini mai yawa, yana da muhimmanci mace ta garzaya asibiti domin bincike da magani mafi dacewa.
Ubangiji yabamu lafiya maidorewa🤲🏻
Ku yimin Sharing din wannan posting din domin muhadu cikin ladan mutaimaki juna Bakidaya.
Masu Bukatar Hadadden Original Magic sabaya powder dinmu da Oil na Hips Breast and kiba munadashi Available Akwai Magungunan Gyaran Breast Hips masu aiki cikin 7dys zakiga Results inshAllah Akwai baby mix food daga wata shida idan kinaso Munada magungunan mata masu kyau akwai sabulan tsarki na Mata da infection flusher available muna tura kayanmu kowane gari kuma muna bada sari kimin mgn ta wannan number (08084726875)_(07062950801)


0 Comments