YADDA AKEYIN HADADDIYAR SOYAYYIYAR TALIYA NA ZAMANI MAI DADI DA KAYATARWA


INGREDIENTS 

  1.  
  2. • Taliya
  3. •Tumatir
  4. •Nama
  5. • Kaza
  6. •Karas
  7. •Koren wake
  8. • ‘peas’
  9. •Magi
  10. • Kori
  11. • Tafarnuwa
  12. •Citta
  13. •Albasa
     

               YADDA ZAKI HADA 

A dora ruwa a wuta, bayan ya tafasa sannan a zuba taliya da gishiri kadan. Idan ta yi tafasa daya sai a tsame. A dora man gyada a wuta sannan a zuba yankakkiyar albasa da yankakken tumatir da jajjagaggen attarugu. A tafasa nama sannan a yayyanka shi kanana sannan a zuba. A zuba magi, kori da garin tafarnuwa da citta sannan a dauko wannan taliyar a zuba ta a ciki a gauraya. A zuba ruwa kadan sannan a rufe bayan mintuna biyar a sauke.

A tafasa kaza ta yi laushi hade da magi da kayan kanshi sannan a soya da man gyada. A soya tumatir da attarugu da albasa. A zuba magi da citta da tafarnuwa. Bayan sun soyu sannan a dauko kazan a cakuda shi a ciki sannan a dora a kan wannan soyayyar taliyar.